Kwamishinar al'amuran mata da bunkasar walwalar jama'a ta jahar Kano Dr.Binta Tijjani Jibril ta ce matsalar ta shafi kowa da kowa
WASHINGTON, DC —
Makonni kusan biyu kenan da ma'aikatar kwamishinar al'amuran mata da bunkasar walwalar jama'a ta jahar kano ta kaddamar da wani shirin fadakarwa a kan miyagun d'abi'un da ke gurbata rayuwar al'umma. Daga kaddamar da shirin Halima Djimrao ta tattauna da kwamishinar ma'aikatar, Dr.Binta Tijjani Jibril, kuma a cikin kashin farkon tattaunawar kun ji Dr.Binta ta yi bayani sosai a kan shirin, kuma ta bayyana abubuwan da ake nufi da miyagun dabi'u har ta bada misalin cewa irin su shaye-shayen kayan sa maye da jirkita kwakwalwa da suka addabi matasa maza da mata har ma da matan aure, da barace-barace, da tallace-tallace, da aikatau da dai makamantan su. To ganin cewa a wasu kasashe idan aka kaddamar da irin wannan shiri na fadakarwa a kan miyagun dabi'u, a gefe guda kuma ana daukan wasu kwararan matakan karfafawa da tallafawa wadanda matsalar yin ta'ammali da miyagun dabi'un ta shafa kai tsaye domin su iya dogaro da kan su, kuma su iya rabuwa da miyagun dabi'un, shi ne Halima Djimrao ta tambayi kwamishinar al'amuran mata da bunkasar walwalar jama'a ta jahar Kanon Dr.Binta Tijjani Jibril, ko sun yi tunanin daukan irin wadannan matakan tallafawa kafin su kaddamar da shirin na fadakarwa?
Your browser doesn’t support HTML5