Kamar yadda ya bayyana shugabannin jama'iyyar na Kano su suka rubutawa majalisar zartaswa ta kasa ta jam'iyyar cewa lokacinsu ya kare don haka a gaya masu ranar da za'a yi sabon zabe da yadda za'a yi zaben. Sun rubuta wasikar ne tun kafin rigimar jam'iyyar ta barke. Amma ba'a yi komi ba sai bayan da rigima ta kunno kai shugabannin jam'iyyar na kasa suka kafa kantoma abun da babu shi a kundun tsarin gudanar da jam'iyyar.
Ambassador Kazaure ya ce idan Bamanga Tukur na son ya rika nada abokanansa kan mukami jam'iyyar PDP yanzu tafi karfin haka.Lokacin nada abokai ya wuce. Dole a bi tsari, a yi zabe kafin kowa ya dare kan kowane mukami. Yanzu maganar ta rincabe a Kano domin an kai shi Ambassador Kazaure kotu da kantoman da Bamanga ya nada da sakataren kantoman da shi Bamanga Tukur. Irin wannan dagulewar ba zata haifar da da mai ido ba.
A halin yanzu babu batun sasantawa sai an yi gaskiya an bi abun da kudun tsarin mulkin jam'iyyar ya ce a yi. Ya ce ana shirin sasantawa amma wadanda basa son jam'iyyar ta gyaru suna dada kawo baraka domin sun san yin sulhu zai kawo masu asara.
Ga karin bayani.