WASHINGTON —
Cibiyar Sasanta Al’umma da Gwamnatin jihar Kano ta kafa da taimakon Hukumar Raya Kasashe ta kasar Burtaniya DFID ta sasanta rigingimu iri iri har sama da dari biyar daga karshen shekara ta 2009 zuwa bana, bisa ga rahoton da wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana.
Wakilinmu Mahmud ya dauko muryar Shugabar Ayyukan Cibiyar a unguwar Kabuga mai suna Barrister Habiba Abdulmummuni Yelwa na cewa idan an je ofishin hukumar za a tarar da magatakarda wanda za a gabatar da korafi gare shi kyauta . Daga nan za a yi nazarin korafin don a tantance ko wa ya kamata a gayyata ko kuma a je wuruinsa; kuma yaushe ya kamata a yi hakan don a cimma maslaha.
Kabiru Mukhtar, wani wanda ya gabatar da korafi dangane da wani cinikin gida da su ka yi sama da shekaru biyu y ace cibihyar ta sa an biya shi cikin kasa da wata guda kuma ba tare da ya biya komai ba. Wani kuma mai suna Abubakar Musa ya ce rigimar fili ce ta sa shi kai kara kuma ga dukkakn alamu ya na gab da samun biyan bukata.