Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Fitsara A Kano


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Gwamnatin jihar Kano ta himmatu ga yaki da duk wata banzar dabi'ar da za ta iya hana jama'a, musamman ma matasa, amfana da ayyukan da gwamnati ke yi, in ji Kwamishiniyar Al'amuran mata.

Ma’aikatar Al’umuran Mata da Walwalar Jama’a ta kaddamar da yekuwa kan illar fitsara da shaye-shaye. Da ta ke bayani wa abokiyar aikinmu Halima Jimrau, Kwamishiniyar Ma’aikatar Dr, Binta Tijjani Jibrin, ta ce har da wasu matan aure masu fama da bala’in shaye-shaye. Ta ce yawan tallace-tallace da barace-barace da aikatau na ‘ya’ya mata, wadanda ya kamata a ce su na makaranta da dai sauransu na daga cikin matsalolin da su ke kokarin magancewa.

Da ta ke amsa tambayar Halima, Dr Binta ta ce dalilinta na tashi haikan don yakar rashin da’ar shi ne dama tun farko sha’anin tarbiyya da inganta rayuwar jama’a da walwalarsu duk hakki ne na hukuma. Ta ce gwamnatin Kano na kokarin inganta rayuwar mutane ta hanyoyi dabandaban amma kuma sai ga munanan dabi’o’I na neman wofinta kokarin gwamnati. Shi ya sa su ka zaburo in ji ta.

Dr. Binta ta kuma ce yanzu haka ana ta kokarin inganta makarantu amma kuma matasa da yawa na shaye-shaye da wasu munanan al’adun da ba za su barsu su nimi ilimin kamar yadda gwamnati ke kokarin ganin sun yi ba. Ta ce wannan fadakarwar za ta fahimtar da jama’a game da illolin dukkannin nau’ukan fitsarar don a amfana da irin ayyukan da gwamnati ke wa jama’a

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00
Shiga Kai Tsaye
.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG