Cikin wani rahoto da kamfanin Google yake fitarwa duk shekara shekara wannan karon akwai maganar karfafa tsaron wayoyinsa na Android yayi.
A cikin rahotan, Google ya ce yana bincikar App dake kan wayoyinsa dake fadin duniya har Biliyan 6 a kullum, domin neman gurbatattun App dake cutar da wayoyin mutane wani lokacin harma da satar bayanan dake kunshe cikin waya.
Kamfanin dai yace yana duba wayoyi kimanin Miliyan 400 a rana, amma dai babu bayanin ko ta yaya yake yin hakan, shin yana duba sune ba tare da masu wayoyin sun sani ba ko kuma masu wayoyin ne ke yi da kansu.
Baki daya dai kowa ya san yadda tsaro yake ga manhajar Android yanzu a duniya, Google dai ya ce cikin shekarar nan ta 2016, wayoyin da suka sami ire-iren gurbatattun App ta hanyar saukar da su ta kundin sauke App na Google Play basu da yawa, amma wadanda ke amfani da wani kundi bana Google ba wajen sauke App na karuwa.
Google dai baya wasa wajen kare harkar tsaron manhajarsa, yana sabunta duk hanyoyinsa domin karfafa tsaro, yanzu haka ma akwai manhajar tsaro da yake amfani da ita mai suna Marshmallow wadda ke baiwa mutane bayani kan halin da wayarsu ke ciki.