Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararriyar Jami'ar YALE Ta Amurka Zata Fara Shirin Matasa Na Summer 2016!


Daya daga cikin jami’o’in da sukayi fici a duniya, “YALE University” ta nan kasar Amurka, ta shirya wani taron karama juna sani, na yara matasa ‘yan makarantar sakandire da suka fito daga kasashen Afrika. Wannan horarswa kyauta ce batare da mutun ya biya ko sisi ba, kuma za’a kawo matasan ne nan kasar Amurka don basu wannan horaswar. A zangon karatu na Rani da ake kira "Summer 2016" a turance

An dai shirya wannan koyarwar ne ga matasa da suke kokarin kammala karatun su na sakandire, da zummar basu horaswa a fannoni daban-daban. Wannan horarwar ta shafi bangarori da dama, duk matashin da ya samu shiga wannan zababbu da zasu halarci koyarwar ta sati biyu, zasu samu damar koyon karatu daga malaman da sukayi fice a duniya.

A cikin jerin kwasa-kwasai da za’a koyar da matasan sun hada da fannin tsangayar kimiyya da fasaha, (Applied Science & Engineering) a turance da Ilimin dangantakar kasa-da-kasa tare da tsaro, (International Affairs & Security) a turance kana da bangaren lafiya da hallittan dan’adam, (Biological & Biomedical Science) a turance da Fasaha da kere-kere, da kasuwanci, haka kuma da bangaren ilimin makamashi da yanayi. (Technology, Innovation, & Entrepreneurship) a turance a turance Akwai bangaren siyasa, tattalin arziki, tare da karatun shari’a(Politics, Law, & Economics) a turance.

Ana bukatar duk wani matashi da ke da sha’awar yin karatu a waddannan bangarorin da ya kokarta aika afilikeshan nashi da gaggawa. Wannan jami’ar zata dauki nauyin kudin jirgi da kuma abincin da otel na duk wanda ya samu shiga, na tsawon kwanakin da zasuyi a nan kasar Amurka. Duk wanda ke da sha’awa sai ya kokarta aika form na shi. Za kuma a samu wannan fom din idan an shiga shafin http://globalscholars.yale.edu haka kuma idan mutun na neman karin bayani ko wata tambaya sai a aika da sako zuwa wannan adireshin global.scholars@yale.edu

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG