Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yariman Kasar Ingila William Zai Karbi Bakoncin Shugaba Obama


A ranar Juma’a 22 ga watan Afrilu 2016, idan Allah ya kaimu, shugaban kasar Amurka Barak Obama da maidakin shi Michel Obama, zasu ziyarci kasar Ingila. Inda ake sa rana zasuyi wani taro na musamman na cin abinci tsakanin shugaban kasar da Yariman birnin Ingila William da uwargidan shi, Duchess Kate.

A rahoton da ya fito daga fadar sarauniyar ingila, suna matukar murna da kuma jiran ranar don taron bakon su na musamman shugaba Obama. Wannan wata muhimiyar ranace a tarihin masarautar ingila. Bayan nan kuma shugaba Obama zai gana da sarauniyar ingila Queen Elizabeth II, don tayata murnar cika shekaru casa’in 90 da haihuwa.

Yariman ingilan da mai dakin shi sun ziyarci kasar india wanda su kaje yawon bude ido, a shekarar 2014, yariman da mai dakin shi sun kama ziyarci kasar Amurka. Inda suka samu ganawa da yara marayu a gidajen marayu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG