Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauyin Sarauta Da Tsarin Rayuwar Malam Bahaushe Shekaru 100 Baya


Malama Balaraba Ramat Yakubu
Malama Balaraba Ramat Yakubu

A shirinmu na nishadi a yau mun sami bakunci wata marubuciya mai kuma shirya fina-finai Malama Balaraba Ramat Yakubu wacce ta shafe shekaru ashiri tana rubuce-rubucen litattafai na Hausa.

Ta ce daga baya sai wata kungiya ta dauki littafin ta inda aka mayar da shi fim daga nan ne sha'awa ta sa har ta fara mayar da wasu littafan ta zuwa fina-finai.

Ta ce halin da ake ciki tana aikin wani fim mai suna "Sauyin sarauta" shirin fim din da aka koma fiye da shekaru 100 bayan aka kuma dubi tsarin rayuwar malam Bahaushe a waccan lokaci.

Ta kara da cewa a wanna fin din babu keke ba Mota ba waya takalma ma babu a kafar mutane haka ake yawo, sitira duk irin ta da aka yi amfani dasu, bayin daurin kirji ne su kuwa matan Sarki Gwado ne da Sakakke.

A fanin tsagumi kuwa, Ali Nuhu, Hafuzu Bello, Kamal Alkali da da Nazifi Asnanic, sun yi wani zama a ranar asabar a garin Kano, da wakilam ofishin jakadanci Amurka domin tattauna yadda Amurka zata taimaka wajen bunkasa sana’ar shirya fin din Hausa.

Adam Zango, wanda dama jakadan MTN, ne yanzu haka yana Lagos, domin daukar wani talla domin mutanen arewacin Najeriya.

XS
SM
MD
LG