Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jerin Kasashe Da Sukafi Kashe Kudi A Wajen Yakin Kasa-Da-Kasa


An kiyasta yawan kudaden da wasu kasashe a duniya suke kashewa a wajen yaki. Da kasashe goma da sukafi kowane kasashe kashe zunzurutun kudi a yaki tsakanin kasa-da-kasa. Kashe kudin wadannan kasashen sun hada da yakin cikin gida da na waje.

Kasar Amurka itace kasa ta farko da tafi kowace kasa a duniya kashe kudi a wajen yakin kasa-da-kasa. Su kan kashe wadannan kudaden ne wajen taimakama kasashen da suke fama da yakin kama karya, ko yakin sunkuru. Kamar yakin kasar Libiya, Afghanistan, Iraq da wanda ake gwabzawa a kasar Syria yanzu haka. Kasar kan kashe sama da dallar Amurka billiyan $596B a shekara, don biyan sojojin ta albashi da siyan makaman yaki.

Kasar China, itace kasa ta biyu da suke kashe sama da dallar Amurka billiyan $214.8B, duk da kashe kudin su, basu yi ko kusa da kasar Amurka ba wajen kashe kudi a yaki. Kasar Saudi Arabia na biye da ita da suke kashe sama da dallar Amurka billiyan $87.2B. Kasa ta hudu kuwa itace kasar Rasha, wanda suke kashe sama da dallar Amurka billiyan $66.4B. Haka kasar Ingila sukan kashe kimanin sama da dallar Amurka billiyan $55.5B. Yawancin kasashen nan biyar duk suna kashe kudaden ne a wajen yaki tsakanin wata kasa da wata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG