Kananan Yara Dake Gudun Hijira Sakamakon Rashin Tsaro Basa Samun Ingantaccen Ilmi - Masana

TASKAR VOA: Ana samun yara masu nuna karfin hali wajen yin azumin watan Ramadana tare da manya, duk da cewa ba wajibi ba ne a kansu

Masana a Najeriya na ganin daga cikin illolin da rashin tsaro ya haifar ga jama'a akwai rashin sanin makomar kananan yara dake gudun hijira, wadanda basu samun ilimi, wanda zai sa su kasance da tsarin rayuwa idan sun girma.

SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da dubban yara su ka yi bankwana da karatu sanadiyyar halin da suka samu kansu ciki na ayyukan ‘yan bindiga.

Tun lokacin da matsalar rashin tsaro ta soma addabar jama'a ake ta samun ‘yan gudun hijira da ke kaurace wa garuruwansu domin tsira da rayukansu.

‘Yan Gudun Hijira

Duk da yake mahukunta na cewa suna kokarin magance matsalolin har yanzu ana ta samun kwararar ‘yan gudun jihira zuwa manyan birane, kamar wadannan da suka fuskanci hari kwanan nan a Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Sun bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali, domin da iyaye da mata da yara duk sun tarwatse suna cikin daji. Mata da kananan yara sune suka fi shiga mayuwacin hali cikin ‘yan gudun hijira, watakila saboda raunin da ke gare su.

YAN GUDUN HIJIRA

Duk da yake abu ne mai wuya a samu tsayayyun alkaluma dake nuna yawan ‘yan gudun hijira a jiha ko karamar hukuma, amma dai gwamnatoci da kungiyoyi dama daidaikun jama'a kan kawo musu tallafi domin saukaka halin da suke ciki kamar yadda shugaban karamar kebbe ta Jihar Sakkwato daya daga cikin yankunan da ‘yan bindiga suka daidaita Lawali Marafa Fakku ya ce a matakin karamar hukuma da ma jiha an saya wa ‘yan gudun hijira kayan abinci da na bukatun rayuwa na yau da kullum.

Yan gudun hijira

Farfesa Bello Badah mai sharhi akan lamurran yau da kullum na ganin cewa rashin samun ilimi abu ne mai illa sosai, domin acewar sa tamkar Bom ne jama'a suke akai wanda idan ya fashe zai shafi kowa, ko wadanda ke ta'addanci yanzu sun fara ne da korafin cewa an fita batun su a can baya, ga rashin ilimi sai zukatansu suka bushe.

Wannan lamarin na iya zama tamkar koma-baya ga kokarin da hukumomin duniya ke yi wajen mayar da yara makaranta musamman a arewacin Najeriya, abinda masana ke ganin cewa da gwamnati da al'umma na da rawar da zasu taka wajen daidaita matsalar tun ba'a soma kokawa da ita ba nan gaba.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Kananan Yara Dake Gudun Hijira Sakamakon Rashin Tsaro Basa Samun Ingantancen Ilmi: Masana.mp3