Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijirar Najeriya A Nijar Sun Samu Ci Gaba A Wasu Kauyuka


Wasu ‘Yan Gudun Hijira
Wasu ‘Yan Gudun Hijira

Kasar Nijar da ke yammacin Afirka ta karbi 'yan gudun hijira sama da 303,000 da masu neman mafaka, mafi yawansu na gudun hijira daga makwabciyarta Najeriya.

A yankin kudancin Maradi, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) da kungiyar agaji ta Save the Children sun kafa sansanoni don taimaka wa ‘yan gudun hijirar su tsira daga kan iyaka tare da rage nauyi a kan al’ummar da suka karbi bakuncinsu.

Sansanin ‘yan gudun hijira na Garin Kaka da ke kudancin Nijar, na dauke da ‘yan gudun hijira kusan 4,000 da suka gujewa tashe tashen hankula daga kungiyar IS da ‘yan bindiga a makwabciyarta Najeriya. Yana daya daga cikin sansanoni uku da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa a yankin Maradi na Nijar tun daga shekarar 2019 a matsayin abin da ta kira "kauyen bada dama".

'Yan gudun hijirar da ke wadannan sansanonin, irin su na farko a Nijar, an kwashe su ne daga kan iyaka, domin kare lafiyarsu, kuma 'yan gudun hijira da mazauna yankin na samun agaji.

Manufar bayar da agaji ga mazauna yankin shi ne a rage musu nauyi daga yawan ‘yan gudun hijira da kuma sassauta duk wani tashin hankali da ka iya tasowa ta hanyar neman albarkatu.

Ana kuma baiwa mata ‘yan gudun hijira kananan kudade don kafa shaguna domin su rika samun abun kulawa da iyalansu.

'Yar Najeriya Hanetou Ali mai shekaru arba'in da biyu da haihuwa ta gudu daga kauyensu shekaru uku da suka gabata da kafarta tare da 'ya'yanta 11 bayan da mayakan IS suka kai hari tare da kashe makwabtanta.

Ta ce lokacin da mayakan suka fatattake su, ita da iyalanta sun gudu. Amma ‘yan bindiga sun kama wani mutum da matarsa, in ji ta, suka yanyanka shi.

'Yar kungiyar Ilaria Manunza ta ce yana da matukar muhimmanci a tallafa wa 'yan gudun hijira kamar yadda ake yi wa 'yan kasar, wadanda ke fuskantar matsin lamba daga sauyin yanayi.

"Mun kuma yi imanin cewa har yanzu yawan masu bada masaukin bakin suma suna bukatar wasu tallafi, don haka ba za mu iya mantawa da yawan wadanda suka karbi bakuncinsu ba, kasancewar sun yi matukar maraba da goyon bayan 'yan gudun hijirar," in ji Manunza. "Saboda haka, ya kamata duk matakan da muka dauka a ko da yaushe su shafi al'ummar 'yan gudun hijira da kuma masu masaukin baki."

Kungiyoyin ba da agaji na fatan 'yan gudun hijirar da ake kira Kauyukan bada Dama za su zama masu dogaro da kansu daga karshe.

Sai dai wasu daga cikin matan ‘yan gudun hijirar sun ce ba za su iya bunkasa sana’arsu ba saboda babu isassun bukatu na ayyukansu a sansanin.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce rikici a arewa maso yammacin Najeriya ya tilastawa ‘yan Najeriya fiye da 80,000 yin hijira zuwa yankin Maradi na Nijar. Kusan ƴan gudun hijira 18,000 ne aka ƙaurar da su zuwa sansanonin uku tare da samfurin Kauyukan bada dama.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG