WASHINGTON, DC —
Ka Kula:
• Kada kayi cudanya da wanda ya nuna alamar cutar, da ya hada da zazzabi mai tsanani, ko jan ido, ko amai ko kuma ciwon ciki.
• Ka wanke hanunka da sabulu a kai-akai musamman karkashin farcenka, idan kuma babu sabulu sai ka rika amfani da ruwan wanke hannu.
• Kayi amfani da gulob lokacin da kake kula da wadanda ke dauke da cutar Ebola.
• Ka dafa nama sosai, ka kuma guji cin naman daji.
• Ka sa rigar kariya da safar hannu duk lokacin da ake taba dabbobi.
• Kada ka taba wanda ya mutu da cutar Ebola.
• In kunne yaji gaggan jiki ya tsira.
* Sako daga cibiyar yaki da cutuka ta kasa da kasa.