Likitocin sun ce sun kira taron manema labaran ne domin su fadakar da sauran ma'aikatan asibiti game da cutar ebola domin su ne mutanen farko dake karo da masu cutar wadan kuma sau tari tana komewa garesu.
Dalilin haka suka ga yakamata su tattara ma'aikatan asibiti su ilimantar dasu game da yadda zasu kare kansu a duk lokacin da muamala ta hadasu da wani dake da cutar domin ba'a san mutane nawa ne za'a sake kawowa asibitocin jihar ba.
Amma likitocin sun koka cewa wani abu mai firgitarwa shi ne gwamnatin jihar bata samar masu wadatattun kayan kariya garesu ba, wato su masu aikin asibitin.
Dr Mutiu Bamidela shugaban likitocin yace basu yadda ba kokadan cewa an dauki hanyoyin karesu daga mummunar cutar ba. Sabili da haka suna rokon gwamnatin tarayya ta yiwa Allah ta basu duk wani abun da zasu yi anfani dashi wajen karesu daga cutar.
A kan jita-jitar cewa an kafa sansanin wadanda suka kamu da cutar a wata anguwa lamarin da yasa wasu suna gujewa wurin Dr Bamidele yace shi bai san da haka ba. Amma akwai wuri na musamman da aka tanada kuma yana aiki gadan gadan. Ya hada da cewa ba wai sun janye yajin aikin da likitoci ke yi ba ne a duk fadin Najeriya, amma sun gudanar da taron ne domin su wayar da kawunan 'yanuwansu, ma'aikatan kiwon lafiya.
Yanzu dai an kwashe makonni shida likitoci na yajin aikin sai abun da hali yayi sakamakon rashin jituwan da suka samu da gwamnatin tarayya.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.