Dalili ke nan da yasa gwamnatocin su keyin duk wani abun da ya dace domin ganin jama'a basu kusanci wajen samun cutar ba.
Daya daga cikin hanyoyin da ake samun cutar ya hada da cin naman daji irinsu gada da gwagwan biri da biri abun da yasa gwamnati ta bada umurnin kauracewa cin namansu har na wani dan lokaci.
Da yake wadannan dabbobin ba gida ake samunsu ba akwai wasu a cikin al'umma farautar dabbobin shi ne sana'arsu. Sabili da haka umurnin bai yi masu dadi ba. Misali kasuwar naman daji dake kan babban titin Isaac Boro a jihar Bayelsa ta zame hoto. Majiya kwakwara ta shaidawa Muryar Amurka cewa ga wanda ya san wurin yau idan ya je abun sai ya bashi mamaki. Kasuwar a da kowane lokaci cike take da mutane musamman ma ranar Lahadi amma yau ta koma wayam daga masu saye zuwa masu sayarwa.
A garin Ibadan kuwa fadar gwamnatin jihar Oyo mata masu sayar da naman dajin suka yi gangami zuwa ofishin gwamnan jihar karkashin shugabarsu Hajiya Riskat Odeyemi domin gwamnan yayi wani abu game da sanarwar da ake ta yayatawa akan cutar ebola. Saidai sun yi rashin sa'a jami'an tsaro basu barsu sun zo gap da ofishin gwamnan ba balantana su samu daman ganinsa.
A jihar Legas bisa binciken da Muryar Amurka ta gudanar hatta masu sayar da nama a gashe, wato balangu ko tsire, sanarwar ta cutar ebola ta shafesu.
Cikin ra'ayoyin da aka tara daga masu sayar da gashe babu wanda aka tambaya yace son barka. Kusan duk mai sayar da gasashen nama abirnin Legas ya koka da cutar ta ebola.
Wani mai sayar da gashi yace bullowar cutar ebola bai fi wata daya ba amma tamkar tayi shekara a wurinsu domin sun shiga mawuyacin hali. Wani yace duka abun da Allah ya kaddara zai sameka sai ya sameka amma tun da suke gashi babu wanda ya taba cewa gashi na kawo wata lallura sai wannan karon da cutar ebola ta bullo.
Babu shakka cutar zata tilastawa mutane su yi ban kwana da cin naman daji. Masu sana'ar kuma zasu rabu da ita domin sai da masu saye ne zasu iya cigaba.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.