Jami’an kiwon lafiya na kara fadakar wa al’umma da kai a kan batun barkewar muguwar cutar Ebola da ta addabi kasashen yammacin Afrika, cutar da yanzu haka tayi sanadiyar mutuwar mutane 4 a Najeriya.
A wata hira da Aliyu Mustapha ma’aikacin muryar Amurka yayi da Dr. Bello Abdulkadir Zaria, likitan ya yi kira da a kara wayar ma al’umma da kai akan wannan cutar, kamar yadda ake kamuwa da ita, alamomin cutar, kariya, maganin ta idana akwai da kuma hanyar dakile yaduwar cutar, don ba jami’an kiwon lafiya ne kawai zasu iya yakar cutar ba sai dai da hadin kan al’umma baki daya. Ya kuma kara bada haske akan alamomin cutar wanda suka hada da masassar mai zafi, ciwon kai, amai, gudawa da aman jini in cutar tayi tsanani.
A makon da ya gabata wasu sun nemi hanyar gargajiya wajen tunkarar wannan cutar, inda aka yada jita-jitar cewa, shan ruwan gishiri da wanka da shi na kariya daga cutar, wanda hakan ya janyo illa sosai ga wasu. Akan batun ne ma Dr. Bello ya kira al’amarin “Jahilci da Rashin Fahimta” don ba masana a fannin kiwon lafiya bane suka bada sanarwar.
Daga karshe likitan ya kara da cewa, yayi imani bin dabi’un tsapta masu kyau kamar wanke hannu, rufe baki in za a yi attishawa da kula da jiki zasu kare mutum daga kamuwa da cutar.