Gwamnan yace majalisar zartaswar jihar ta bada umurnin cewa kwamishanonin noma da na kiwon lafiya da sauran wadanda abun ya shafa su je inda ake sayar da irin wannan naman mako mai zuwa su kawo masu rahoto.
Bayan an kawo rahoton mako mai zuwa gwamnati zata dauki matakan da suka dace a jihar Kano. Yace idan naman dabbobin daji zai cutar da mutanen jihar gwamnati zata hana sayar da shi a duk fadin jihar. Ban da haka zasu fadawa mutanen Kano cewa idan sun fiita daga jihar sun ga ana sayar da naman daji kada su kuskura su saya. Idan kuma mutum ya ki ya kamu da cutar ebola to shi ya jiwoma kansa. Duk abun da gwamnati ta gani yana da hadari ba za'a yi shakka ko tsoron gayawa mutane a daina yin sa ba.
Bayan batun ebola gwamnan yayi tsokaci game da sabon daftarin kundun tsarin mulki da aka ce an ga bullarsa a zauren taron kasa a Abuja. Gwamnan Kwankwaso yace duk maganar sabon kundun tsarin mulki duk domin a cigaba da mulki ne. Bayan Goodluck Jonathan yayi shekara biyu yana mataimakin shugaban kasa, yayi shekara biyu yana shugaban kasa, yanzu kuma yana yin shekara hudu shugaban kasa, yana son duk wadannan a turasu gefe daya cewa bashi yayi ba. Yanzu yana son ya fara sabon muilki a 2015 yayi shekara takwas.
Gwamna Kwankwaso yace ba wannan ba ne matsalar. Matsalar ita ce shin a yi shekarun nan takwas a hakan da ake tafiya. Kowa ya damu. Kowa yana cikin matsi. Akwai matsi a arewa akwai a kudu. Ana kashe rayuka koina ana sace sacen mutane koina. Shugabanci kuma bai damu ba, bai ma san ana yi ba. Wanda kuma ya fada shi ne mai laifi. Yace shi dinnan da yake fada a wurin shugaban kasa laifi yake yi. Idan an ce yara dari biyu sun bata a fito dasu sai a ce kayi laifi. Sai yace a manta dasu. Babu damuwa wadannan yara ne. An kwashesu amma kada ku yi magana za'a kawosu.
Rahotanni na nuni da cewa muddin daftarin ya samu wucewa a zauren taron mataki na gaba shi ne kuri'ar neman raba gaddama tsakanin 'yan Najeriya. Sai dai gwamna Kwankwaso yace "ai inda za'a ce an tashi majalisa an kawoshi Kano in muka yi masa wani duka a Kano ma ko tsallakawa ya fice ya dubi wani guri ba zai yi ba. Ai shi ba haka yake so ba. Kuma ko zagawar za'a yi dashi muga inda za'a bullo mana su kawo mana Kano wani yace ya zo rafaranda a Kano ya zo yaji ra'ayin mutane. Zai gane a rayuwarsa cewa idan bai taba kuskure ba ranan yayi. Muna da constitution ana yi kawai shugabanni sun kasa komi. Basu iya ba kuma basa son su koya"
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.