Hadaddiyar Daular Larabawa ta Dage Haramcin Bai wa 'Yan Najeriya Biza

Kamfanin jiragen saman Emirates

A wata gagarumar nasara da aka samu a fannin diflomasiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a hukumance ta dage haramcin biza da ta kakabawa 'yan Najeriya.

Wannan mataki ya biyo bayan wata muhimmiyar ganawa da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi da shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al Nahyan a Abu Dhabi.

Ganawar shugaban kasar Bola Tinubu na Najeriya da shugaban kasar UAE Mohamed bin Zayed Al Nahyan a Abu Dhabi.

Yunkurin da Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi na ɗage takunkumin hana tafiye-tafiyen biza ya nuna wani sauyi a dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Nan da nan, matafiya na Najeriya za su iya sake ziyartar UAE ba tare da takunkumin da aka saka a baya ba.

A yanzu kamfanonin jiragen saman na Etihad da na Emirates za su dawo da jigilar tashi da saukar jiragensu zuwa Najeriya ba tare da sanya wa gwamnatin Najeriya wasu wajibai na kudi nan take ba.

Ganawar shugaban kasar Bola Tinubu na Najeriya da shugaban kasar UAE Mohamed bin Zayed Al Nahyan a Abu Dhabi.

Sanarwar wadannan yarjejeniyoyin ta fito ne ta wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban ta United Arab Emirates (UAE) bayan ganawa da Tinubu ya yi da takwaran aikinsa Al Nahyan a ranar Litinin.

Bugu da kari, wannan Yarjejeniya ba ta ƙunshi biyan wani kuɗi na nan kusa ba tsakanin ƙasashen biyu, wacce ta shafi batun wasu miliyoyin dalolin kudade da gwamnatin Najeriya ta riƙe wa kamfanonin jiragen na kuɗin tikiti.

Rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ya samo asali ne tun daga lokacin annobar Korona, inda kasar UAE ta dakatar da baiwa matafiya daga Najeriya biza.

Tattaunawar da aka yi tsakanin Shugaba Tinubu da Shugaba Al Nahyan kawo karshen wannan rikici tare da kuma haifar da samar da wani tsari na saka jari mai tsoka a cikin tattalin arzikin Najeriya.

Wadannan jarin da suka kai biliyoyin dalar Amurka, za su shafi bangarori daban-daban da suka hada da tsaro da noma, kuma ana sa ran za su kawo ci gaban tattalin arziki da ci gaban Najeriya.

A jawabinsa, shugaba Tinubu ya bayyana jin dadinsa ga kyakykyawar fahimta da ya samu daga shugaban kasar UAE da kuma yadda suke da niyyar inganta dangantakar kasashen biyu.

~ Yusuf Aminu Yusuf