Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Emirates Na Shirin Rage Zuwa Najeriya


Jirgin Emirates na Dubai
Jirgin Emirates na Dubai

A cikin wata wasikar da ta aike wa gwamnati, wadda kamfanin dillancin labaran Reuters ta gani, kamfanin jirgin Emirates na Dubai na shirin rage zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya, sakamakon matsalar maido da kudaden shiga daga kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afurka.

Wasikar ta ce kamfanin jirgin na Emirates na shirin rage yawan zuwa Legas daga 11 zuwa 7 daga tsakiyar watan Agusta, inda ya ce dala miliyan 85 dinsa ya makale a kasar a watan Yuli, adadin da ke ta karuwa da dala miliyan 10 a kowane wata.

Masu lura da al'amuran masana'antu sun ce karin kamfanonin jiragen sama za su iya yin koyi da hakan idan babban bankin kasar da ke hana samun kudaden waje don magance matsalar karancin dala, bai magance matsalolin kamfanonin jiragen ba.

“Ba mu da wani zabi illa daukar wannan mataki, domin rage hasarar da Emirates ke ci gaba da yi sakamakon toshewar kudade a Najeriya,” in ji kamfanin a wata wasika da ya aike wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ranar 22 Yuli, 2022.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama bai amsa bukatar yin sharhi ba.

Emirates, a cikin wata sanarwa da ta aika ta imel, ta ce matsalar maido da kudade na yin tasiri a kasuwancinta a Najeriya, kuma kokarin da ake na shawo kan matsalar bai samu nasara ba.

Kamfanin Emirates bai ce komai ba kai tsaye kan wasikar kuma ya ce ya na fatan ci gaba da aiki da cikakken jadawalin.

Najeriya, wace ke samun kusan kashi 90% na kudaden waje daga man fetur, tana fama wajen samar da shi saboda satar man ta bututu da kuma rashin zuba jari na tsawon shekaru.

A cikin irin wannan takunkumin hana musaya na kasashen waje a shekarar 2016, kamfanonin jiragen sama da dama sun rage zirga-zirgar jiragen sama sannan kuma kamfanonin Iberia da United Airlines sun daina tashi zuwa Najeriya gaba daya. Sai dai jirgin United Airlines a shekarar da ta gabata ya sake kaddamar da zirga zirgar Najeriya, amma har yanzu Iberia bai dawo ba.

~ REUTERS

XS
SM
MD
LG