Kamfanin Apple Na Jayayya Da Gwamnatin Amuraka

Apple CEO Tim Cook

Kamfanin kera kwamfuta da wayoyin hannu na zamani Apple, ya hau kujerar naki bayan da gwamnatin Amurka ta umarce shi da ya bude manhajar sa ta wayar iphone, domin baiwa jami’an tsaron FBI damar bincikar wayar ‘dan bindigar nan da ya kashe mutane 14, a harin nan na jihar California cikin watan Disamba.

Ranar Laraba ne shugaban kamfanin Apple, Tim Cook, ya kafe wata budaddiyar wasika ga miliyoyin masu amfani da kayan Apple, yana mai nunin cewa kamfanin zai kalubalanci hukuncin da kotu ta yanke na bude manhajar wayar iphone, wanda hakan zai kashe manufar tsaron da suke kokarin ganin sun samar ga wayoyinsu.

Tim cook ya ci gaba da cewa gwamnati na son mu yi kutse wa abokan cinikin mu, kuma mu rushe tsaron da muka gina na tsawon shekaru, ciki kuwa har da miliyoyin Amurkawa don kare su daga masu kutse a yanar gizo.

Daga karshe Cook yace Apple ba ya tausayawa ‘yan ta’adda, kuma ya tabu matuka ga harin da aka kai garin San Bernardino, na jihar California a shekarar da ta gabata, wanda haifaffen Amurakan nan Syed Rizwan Farook da matarsa Tashfeen Malik suka kai.