Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Yan-Najeriya Masu Taka Rawar Gani A Fadin Duniya


Nazifi Nuhu
Nazifi Nuhu

Nazif S. Nuhu dan asalin garin Kano ne, a Nigeria. Ya fara karatun shi a makarantar firamare a Airforce Primary School, da ke jihar kano. Daga bisani ya tafi makarantar gaba da firamare ta Hassan Gwarzo Secondary School, da ke jihar Kano. A shekara 2004 Nazif, ya fara karatun digri na farko a bangaren kerekere “Civil Engineering” a Jami’ar Bayero da ke kano. Daga bisani ya koma makarantar koyon aikin jirage a kasar daular larabawa “United Arab Emirates- Dubai” wadda aka fi sani da “Dubai Aerospace Enterprise University”

Nazif, ya koma jami’ar “Embry Riddle Aeronautical University” a garin Daytona Beach, jihar Florida ta kasar Amurka. A shekara ta 2011 ya samu digrin shi na farko a fannin kimiyar jiragen sama wanda aka fi sani a turance “Bsc Aeronautical Science.” A shekara ta 2014 Nazif, ya kammala karatun digiri din shi na biyu a fannin kimiyar jiragen sama wanda aka fi sani da “Msc Aeronautical Science” a jami’ar “Embry Riddle Aeronautical University.”

A shekara ta 2015, Nazif, ya fara karatun digirin-digirgir bangaren sarrafa jiragen sama wadda aka fi sani da “PhD in Aviation Science” a jami’ar Florida Institute of Technology, a garin Melbourne dake Jihar Florida a kasar Amurka, wadda a halin yanzu yana shekarar shi ta biyu.

Nazif, ya samu shedar daukaka da dama a fanin karatun shi na harkar kimiya da sarrafa jiragen sama. Yana fatan bayan ya kammala karatun sa, zai koma gida Najeriya, ya taimakawa kasar shi a fannin harkar sarrafa jiragen sama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG