Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Ne Ke Aikin Bincikar Duk Sakonnin Yanar Gizo A China


‘Yan sandan kasar China sun dauki dubban yara matasa domin su kula da yadda sakonni ke gilmayya ta yanar gizo.

Kamar yadda Babban kungiyar ‘Yan jarida na kasa da kasa dake kasar ta China tace, yanzu haka matasan da yawan su ya haura Dubu Uku ne suke aikin sa kai na sanar da hukumomi irin bayanan da suka tattara ta hanyar sadarwar zamani kuma sun kwashe shekaru biyu ne suna gudanar da wannan aikin.

A cikin tsawon wannan lokacin rundunar ta ‘yandsanda sun aike da sakon gargadi ga mutane da yawan su yakai 8,400, kana sun goge ko kuma sakonnin da yawan su yakai dubu dari biyar gittawa ta duniyar gizo kana sun goge wasu a kalla Dubu Tara.

Kamar yadda kanfanin dillacinlabarai na kasar ta China Xinhua ya ruwaito, yace cikin maasu wannan aikin kaso 80 daga cikin su an haife su a tsakanin shekarar 1980 da 1990, kuma yawancin su suna da ilmin zamani mai zurfi.

Mahukuntar kasar ta China suka ce wannan aikin ya samar da bayanan dakile ayukan assha har sama da Dubu 15, iri daban-daban.

XS
SM
MD
LG