Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani Da Wayar Hannu Wajen Hasashen Girgizar Kasa


Emergency rescuers remove a body found in a collapsed building from an earthquake in Tainan, Taiwan, Feb. 7, 2016.
Emergency rescuers remove a body found in a collapsed building from an earthquake in Tainan, Taiwan, Feb. 7, 2016.

Wayoyin hannu na zamani ka iya zama na’urar hasashen girgizar kasa nan gaba, godiya ga wata sabuwar hanyar ratse da waya da za a iya dangwalawa ta waya, wato App a turance, wadda aka kaddamar ranar Juma’a, ita dai wannan App zata iya hasashen girzizar kasa kafin faruwa ta kuma ceci ran masu amfani da ita, ta hanyar gujewa daga yankunan.

Ita dai wanna App mai suna MyShake, yanzu haka tana nan ga mutanen dake amfani da wayoyi masu manhajar Android. Ga duk wanda yake da ita zai samu duk wani gargadi idan a yankin da kake na cikin hatsarin afkuwar girgizar kasa, zakuma ta fada maka wacce irin girgiza ce, harma da yawan mutanen dake yankin. Bada dadewa ba zata fara kirgan lokaci kafin faruwar girgizar kasar.

Wadanda suka kirkiro wannan App din sunce, zata iya taimakawa al’umma da gargadi ba tare da sun mallaki na’urorin da ake amfani da su abaya ba.

A cewar Richard Allen, daya daga cikin wanda suka kirkiro wannan fasaha, yace MyShake ba zata maye tsofaffin na’urar da ake amfani da ita ba a baya musammam ma kamar wadda masana ma’adanan kasa na Amurka ke amfani da su.

Amma yace wannan App zai yi aiki cikin sauri wajen fitar da gargadi dama sahihancin bayanai a yankunan da ke da na’urai da ake amfani da su a baya. Zama ta iya bayar da gargadi mai amfani ga kasashen da basu da ire iren wadancan na’urorin.

XS
SM
MD
LG