Shafin Facebook na ci gaba da shiga zukatan ‘yan Najeriya da ma sauran kasahen Afirka, cikin wasu shirye shirye na hadin gwiwa a nahiyar.
Cikin wata sanarwa da aka fitar kwanan nan, Facebook ya sanar da cewa yana bikin murnar ranar abokai a Najeriya, bayan da ‘yan Najeriya kimanin Miliyan 16 ke ziyartar shafin Facebook a kowanne wata. Baki daya masu shiga shafin, na shiga ne ta hanyar yin amfani da wayar hannu.
A kowacce rana mutane Miliyan 7.2 ne ke shiga shafin Facebook, Miliyan 7 daga cikin su suna shiga ne ta wayoyin hannu. Cikin shekaru biyar da suka gabata, al’ummar dake amfani da shafin Facebook na duniya sun ninka yawansu, haka zalika al’ummar shafin sadarwar dake Najeriya na ci gaba da karuwa.
A cewar mataimakin shugaban Facebook Nicola Mendelsohn, “A gurin mu, bikin murnar ranar abokai a Najeriya, shine jin labarai daga al’ummar Facebook, ta yadda shafin zai kara habaka da hada mutane ta ko ina. Mun samu ci gaba sosai cikin shekarun da suka gabata. A Najeriya yanzu ma muka fara.”
Shima mai kula da nahiyar Afirka na kamfanin Facebook, Nunu Ntshingila, cewa yayi cikin wannan shekara zamu tsunduma da hada kai da ‘yan kasuwar Najeriya, domin kawo ci gaba ga fasahar wayoyin hannu.
Yanzu haka dai ‘yan Najeriya na amfani da Facebook fiye da duk wasu kafofin sadarwa a yanar gizo, haka zalika kwatankwacin kashi 77 cikin 100 na ‘yan kasar an amfani da wayoyin hannu ne wajen shiga yanar gizo.