Kamaru Ta Dauki Matakin Dakatar Da Masu Shirin Raba Kasar

Daruruwan matasa na maci kan tituna domin neman ballewa daga Kamaru.

Kamaru ta girke dubban dakarunta a yankunan Arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar, sassan kasar masu magana da harshen turancin sarauniya, domin dakatar da shirye shiryen da yan aware ke yi na kaddamar da ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba watau ranar lahadin nan.

Kafin wannan ranar matasa sunyi watsi da kiran da yan siyasa da kuma shuwagabannin al’umma sukayi na zaman lafiya, matasan suna kai hare hare kan gine-ginen gwamnati da kuma sojoji, da kuma kada tutar da suka ce ta sabuwar kasar su ce.

Kimanin mutane 700 aka sarin su matasa ne suka rika ihu suna kai hari kan gine ginen gwamnati da ofisoshin yan sanda a garin Ekok dake kan iyakar kasar.

Sunyi kokarin tsallakawa cikin Najeria ta Jihar Enugu domin sanarwa da jami’ai cewar an kafa sabuwar kasa, amma jami’an shige da ficen Najeriya suka hana su shiga.

Yan awaren sunyi alkawarin tabbatar da yancinsu ne a ranar 1 ga watan Octoba kuma sun ayyana wani mai suna Juliuis Ayuk Tabe wanda ke gudun hijira a matsayin shugaban su.