A Jamhuriyar Nijar 'yan adawa sun zargi gwamnatin kasar da yin watsi da talakawa musamman na karkara.
Alhaji Dange Na Mai Hula kusa a jam'iyyar MODEN Lumana Afirka ta Hama Amadu reshen birnin Konni yana mai cewa gwamnatin ta yanzu bata sa jama'an kasar gabanta ba. Batun wai ta damu da talakan Nijar bai ma taso ba. 'Yan tsiraru ne suke gudanar da gwamnatin.
Dangane da ko maganarsa ta adawa ce sai yace ai su basa adawa domin 'yan siyasa dake jam'iyyun adawa zaune suke lafiya. Babu mai jin motsinsu balantana hayaniya. Babu cecekuce cikinsu.
Mai Hula yace shugaban kasar yanzu yayi adawa. Lokacin da baya mulki komi aka yi sai ya koka, ya soki lamirin gwamnati da kakkausan lafazi. Duk wata guda sai ya hadu da shugaban kasa.
Sai dai a cewar Alhaji Danbaba Mamman Ceni kakakin reshen birnin Konni na jam'iyyar PNDS mai mulki yana cewa 'yan adawar basu da labarin kasar Nijar saboda ba kasar suke so ba. Yace gwamnatin yanzu ita ce ta fi kowace gwamnati taimakawa talakawa.
Ga rahoton Haruna Mamman da karin bayani.
Facebook Forum