Kungiyar kamfanonin matasa masu sarafa kaya ta bude kasuwar baje koli da zummar karawa matasan kwarin gwuiwan cigaba da ayyukan da suka sa gabansu domin bunkasa tattalin arzikin kasarsu.
Kasuwar ta samu halartar kananan kamfanoni da masana'antu. Kani Habibu Kadaure dake cikin shugabannin kungiyar yana mai cewa "tana yiwuwa kana da hali da dabaru na sarafa abubuwa da yawa amma baka da mutanen dake kama maka don a sayar da abubuwan". Inji Kadaure sun fahimta cewa duk irin abun da gwamnati zata yi idan babu bunkasar tattalin arziki ya zama banza. Yana cewa dole ne a ba bunkasa tattalin arziki mahimmanci.
Bayan zagayawa kasuwar shugaban hukumar bunkasa harkokin kasuwanci ta kasar Nijar Alhaji Musa Sidi Muhammed ya bayyana cewa hukumomi zasu dauki matakan kare matasan daga masu satar fasaha. Yana cewa idan manyan kamfanoni suka samu fasahar suna iya dauka su je su sarafasu su bar matasan da hamma kawai. Za'a basu kariya da zai hana wani yayi anfani da fasaharsu ba tare da izininsu ba. A cewarsa duk duniya gwamnati ce take kera 'yan kasuwarta. Ya kara da cewa duk wani babban kamfani bai kamata ya yi aiki a Nijar ba sai an hadashi da wani karami.
To sai dai matasan na cewa cigaban kamfanoninsu da masana'antunsu na bukatar magance wasu matsalolin na daban. Suna son gwamnati ta tsaya masu a bankuna su taimakawa duk wani karamin kamfani ko wata masana'antar matashi da aka tabbatar zata iya sarafa kaya da inganci da zai habaka tattalin arzikin kasa. Idan ayyukansu sun bunkasa gwamnati zata samu haraji.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum