Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IS Kan Iya Mayar Da Libya Tungarta - Kwararru


Wasu dakarun Libya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Sirte, Libya, Agusta. 4, 2017.
Wasu dakarun Libya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Sirte, Libya, Agusta. 4, 2017.

Rahotanni daga Libya da yaki ya yi wa katutu, sun nuna cewa, idan ba a yi hattara ba, mayakan kungiyar IS da ke samun koma baya a Syria da Iraqi, kan iya kaura zuwa Libya domin neman mafaka.

Jami’ai da kwararru sun yi gargadin cewa, yayin da mayakan IS ke samun koma baya a yakin da suke yi a Syria da Iraqi, akwai yiwuwar kungiyar ta maida Libya da yaki ya daidaita a matsayin sabuwar matattararta.

Siddiqi al-Soor, wanda shi ne mai shigar da kara kan koken jama’a a Birnin Tripoli, ya fadawa manema labarai cewa, mafi yawan mayakan kungiyar ta IS a kasar na gudanar da ayyukansu ne daga wata runduna da suka kafa a yankin rairayin hamada, bayan da aka fatattake su daga tungarsu dake Sirte a bara.

A l- Soor ya kara da cewa, mayakan kungiyar da ke yankin rairayin hamadan, suna karkashin jagorancin Abdul Qader al Najdi dan kasar Iraqi, wanda aka fi sani da Abu Mo’az Al Tikriti, wanda yake samun taimakon shugabannin kungiyar ta IS Mahmoud Al Bur’si da Hashim Abu Sid.

Ya kuma kara da cewa, hukumomin Libyan, sun samu wadannan bayanai ne daga wani mayakin kungiyar ta IS da aka raunata aka kuma kama, bayan wani harin sama da dakarun Amurka suka kai a yankin Wadi Skir a makon da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG