Hukumomi daga arewacin Jamhuriyar Nijar sun yi karin bayani game da harin da aka kaiwa kasar ranar Asabar da ta gabata a lokacin da wasu mutane da ba'a tantance ba suka farma jami'an tsaro dake yawon sintiri
Harin ya haddasa rasuwar mutane hudu kamar yadda shugaban gundumar ya shaidawa manema labaru. Alhaji Nafalla yana mai cewa wata mota ce akorikura kirar toyota mai launin ruwan toka ta zo daidai da inda jami'an tsaro suke ta bude masu wuta.
Nan take mutane uku suka mutu, biyu suka jikata amma na hudun ya cika ne a asibiti.
Harin an kai ne a gap da garin Asamaka dake kan iyaka da kasar Algeria. Bayan harin jami'an tsaro sun bada umurnin a bi sawun maharan har cikin kasar Algeria domin a farautosu.
Jami'an basu ga kowa ba amma ana cigaba da daukan tsauraran matakai da hukuma ba zata iya bayyanawa 'yan jarida ba.
Ga rahoton Haruna Bako da karin bayani.
Facebook Forum