A ranar 22 ga watan Mayu na shekarar 2023 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a wancan lokacin, gabanin mika mulki ga sabon shugaba ya kaddamar da matatar man Dangote da ke unguwar Lekki a birnin Legas.
Matatar da ta lakume biliyoyin dalar Amurka wajen gina ta na da karfin sarrafa gangar danyen mai 650,000 a kowacce rana, bayan haka za ta samar da guraban ayyukan yi ga dubban ‘yan Najeriya.
Dokoki da ka’idodin sarrafa albarkatun mai na Najeriya, sun yi tanadin cewa tilas ne kamfanonin da ke aikin hakar danyen mai a kasar su samar da shi ga matatun cikin gida kafin su saida wa na ketare.
Sai dai mahukuntan matatar ta Dangote na kokawa kan rashin samun danyen man da su ke bukata daga cikin gida.
“Abin da ke faruwa a yanzu shi ne, ana hako man ya fita, mu kuma muna zuwa wata kasar mu sayo irinsa a kawo shi Najeriya don a tace, a cewar Alhaji Rabi’u Abdullahi, babban jami’in cinikayya na rukunin kamfanonin Dangote.
Ya kara da cewa, a watan Satumba da ke tafe, su na bukatar kago 15 na danyen mai amma kago 5 kadai zasu iya samu, “ka ga dole ne mu je mu nemo sauran ragowar a cewarsa.
Yayin mamatar danyen man ta Dangote ke kokawa kan rashin samun isasshen danyen mai domin sarrafawa, a baya-bayan nan an ji shugaban hukumar kula da cinikayyar albarkatun mai ta Najeriya Alhaji Faruk Ahmed na aibata man da matatar ta Dangote ke tacewa, yana mai cewa ba shi da nagartar da ta dace, al’amarin da mahukuntan matatar man suka musanta.
Masana harkokin tattalin arziki na fashin baki game da illolin kalaman shugaban hukumar kula da cinikayyar albarkatun mai ta Najeriya ga makomar tattalin arzikin Najeriya.
“Saboda irin wadannan kalaman, yanzu zai yi wuya wani ya zo Najeriya zuba hannun jari, idan ma da gaske ne to kamata yayi a sanar da gwamnati, a cewar Dr. Abdulsalam Kani, malami a fannin koyar da harkokin tattalin arziki a jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano. Ya kara da cewa furta irin wadannan kalaman tamkar kwancewa kasar zane a kasuwa ne.
Yayin da matatar ta Dangote ke fama da kalubale da hukumomin Najeriya, mahukuntan kamfanin sun ce a watan Agusta fetur din da matatar ke tacewa zai bayyana a kasuwannin kasar.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5