Tsarin aikin ranaku hudu a mako da gwamnatin jahar Kaduna ta sanar dai ya fara ne daga Larabar nan wato daya ga watan sha biyu saidai kuma hutun ranar Juma'a da za a fara daga wannan mako bai shafi ma'aikatan lafiya da na ilimi ba, inji daya daga cikin ma'aikatan ofishin yada labaru na gidan gwamnatin jahar Kaduna, Malam Abdallah Yunus Abdallah.
Sanarwar wannan sabon tsarin aiki ke da wuya sai kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN, reshen jahar Kaduna ta ce matsalar tsaro ce damuwar al'umma ba rage ranar aiki ba, abun da ya sa wasu jami'an gwamnatin zargin kungiyar da saka addini.
Sai dai shugaban kungiyar Kiristoci a jahar Kaduna, wanda kuma shine mataimakin shugaban ta na jahohin Arewa, Rabaren Joseph John Hayeph, ya ce wannan gurguwar fahimta ce.
Karin lokacin tashi aiki daga karfe hudu da aka saba zuwa biyar na yamma cikin wannan sabon tsarin aiki kuma ya sa mai sharhi kan al'amuran yau da kullun, Alhaji Abubakar Umar Aliyu, ya ce ba rangwame ake nemar wa ma'aikatan ba.
Gwamnatin jahar Kaduna dai ta ce sai a watan Janairun sabuwar shekara za a kammala aikin maida wannan tsari ya zama doka, amma kuma daga ranar Juma'ar wannan mako ma'aikatan za su fara wannan hutu don kara samun lokaci da iyali da kuma komawa gona.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5