Joseph Kabila Ya Fara Wa'adi Na Biyu

Shugaba Joseph Kabila, na Jamhuriyar Demokuradiyyar kwango

Mr. Kabila ya yi rantsuwar kama aiki yau Talata a Kinshasa, bayan zaben da aka gudanar watan jiya da masu sa ido na kasa da kasa suka.

An rantsar da shugaban kasar Damokuradiyyar Jamhuriyar Kwango Joseph Kabila domin wa’adin mulki na biyu, yayinda shugaban ‘yan hamayya Etienne Tshisekedi yake ci gaba da gabatar da kanshi a matsayin shugaban kasar na zahiri.

Mr. Kabila ya yi rantsuwar kama aiki yau Talata a Kinshasa, bayan zaben da aka gudanar watan jiya da masu sa ido na kasa da kasa suka ce yana cike da kura kurai a lokacin gudanar da zaben da kuma kirga kuri’u.

Mr. Kabila ya bayyana cewa, babu wata tantama dangane da sake zabenshi, yayinda jami’an zabe suka ce ya sami gagarumin rinjaye.

Sai dai Tshisekedi ya bayyana kin amincewa da sakamakon zaben da yace an tafka magudi ya kuma ayyana kanshi a matsayin shugaban kasa, yayinda yace zai dauki rantsuwar kama aiki ranar jumma’a.

Amurka ta bayyana zaben a matsayin wanda yake cike da kurakurai. Mr. Kabila ya yi kira ga Tshisekedi ya bi tsarin da doka ta shinfida wajen kalubalantar zaben.

Aika Sharhinka