Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Duniya Ta Samu Thomas Lubanga Da Laifi


Thomas Lubanga a kotu lokacin da alkalai ke yanke masa hukumci
Thomas Lubanga a kotu lokacin da alkalai ke yanke masa hukumci

Tsohon madugun tawayen Kwango ya zamo mutumin farko da wannan kotu ta taba kamawa da laifi tun kafa ta shekaru 10 da suka shige

Babbar kotun bin bahasin manyan laifuffuka ta duniya ta yanke hukumcinta na farko tun kafa ta shekaru goma da suka shige, inda ta samu madugun mayakan Kwango, Thomas Lubanga da laifin sanya yara kanana cikin aikin soja.

Alkalin da ya gabatar da hukumcin yace dukkan alkalan sun yarda cewa shaidar da aka gabatar, ciki har da hoton bidiyo da bayanan wadanda suka gani suka kuma ji, ta nuna cewa Lubanga da mukarrabansa, da saninsu suka sanya yara ‘yan kasa da shekaru 15 aikin soja.

Alkalin yace Lubanga ya dauki wadannan yara ne domin suyi yaki ma bangaren soja na kungiyarsa mai suna Union of Congolese Patriots a lokacin yakin basasar Kwango ta Kinshasa a shekarun 2002 da 2003.

Za a ci gaba da tsare Lubanga har zuwa lokacin da za a fadi hukumcinsa a wani zaman kotun a nan gaba. Yana iya fuskantar hukumcin daurin rai da rai, amma yana da damar daukaka karar samunsa da laifin da aka yi a yau din.

Lubanga shi ne mutumin farko da aka yi shari’arsa a gaban wannan kotun dindindin da aka kafa domin yin shari’ar wadanda ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki. An kafa kotun a shelarar 2002, aka kuma fara shari’ar Lubanga a shekarar 2009, shekaru uku a bayan da aka kama shi.

XS
SM
MD
LG