Jiya Lahadi sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Yemen

Shugaban kasar Yemen Abed Rabbo Mansour Hadi

Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a tsakar daren jiya Lahadi a Yemen tare da daukar alkawarin tsawawa akan wannan maslaha daga bangarorin biyu. Tsagaita wutar na zuwa ne da nufin ya zama sharar fagen nasarar zaman sulhuntawar da za a yi a Kuwait ranar 18 ga watan Afrilun nan.

Rundunar taron dangin Larabawan da Saudi ke jagoranta sunce zasu mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar kamar yadda Shugaba Abd-Rabbu Manosur Hadi ya bukata, amma fa sun ce suna da ‘yancin maida martani ga duk wani farmaki da ka iya biyo baya.

Suma ‘yan tawayen Shi’ar Houthi da Iran ke marawa baya sun ce za su mutunta tsagaita wutar, amma suma zasu yi raddi idan aka takale su. An dai sami rahotannin barkewar fadace-fadace gab da fara aikin yarjejeniyar tsagaita wutar, wanda har rahotannin ke nuna akalla an kashe mutane 20.

An dai sami kasa kai labarin yunkurin tsagaita wuta da dama a Yamal din, inda a yanzu haka fararen hula ke fatan Allah yasa wannan karo yarjejeniyar ta yi karko. ‘Yan tawayen Houthi dai tun a shekarar 2014 suka mamaye birnin Sanaa, inda hakan ta tilastawa Shugaba Hadi tsallakewa zuwa Saudiyya neman mafaka.