A hira da muryar Amurka , darektan ya ce wayanda aka kwason akasarin su dalibai ne da suka ketare zuwa kasar Romania domin tsira da yakin na Rasha da Ukraine. Jami'in na NEMA yace akwai wani jirgin da ake sa ran zai sauka Najeriya da yanmacin yau jumma'a dauke da yan Najeriyan.
Game da matakan da hukumomi Najeriya suka dauka domin jin dadin daliban kuwa yace shugaban kasa ya umarci a baiwa duk wanda aka dauko dala 100 na amurka, kwatankwacin Naira dubu 50 domin guziri da kudin mota zuwa garuruwan su na asali. Yace a wannan karon ba'a ajiye kowa a sansanin 'yan gudun hijirah ba. Game da zargin da ake yi cewar jiegin da ake jigilar 'yan Najeriya yayi kadan kuwa, Alhaji Garga yace akwai jirage da dama da aka ware domin wannan aiki kuma dukkansu na daukan fasinjoji da dama, kamar wannan da ya dawo da su yana daukan mutane fiye da 400 ne, kuma haka za su yi ta jigilar har sai sun kammala.
Kawo yanzu dai jami'in na NEMA yace filin jirgin saman abuja ne kacal aka ware domin wannan aikin jigilar sabanin Lagos da Abuja da tun farko hujumomi suka ce za'a yi anfani da su.
Yanzu haka dai 'yan Najeriya fiye da dubu hudu ne ke karatu a Ukraine, kuma akasarin su sun tsallaka zuwa kasashen dake makabtaka da Ukraine irin su Romania da Poland domin samun mafakar wannan yaki daya goce tsakanin Rasha da Ukraine.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5