JIhar Adamawa Zata Kafa Hukumar Da Zata Ke Saka Ido Kan Gururuwan Da Aka Kwato

'Yan gudun Hijira

Yayin da hankula ke kara kwantawa a garuruwan da aka kwato daga hannun yan Boko Haram, yanzu haka hankula sun karkata game da makomar wadanda ke komawa garuruwan ta fuskar yadda zasu sami abinci da kuma sauran ababen more rayuwa.

Daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya fi shafa jihar Adamawa, ‘yan majalisar dokokin jihar sunyi wata doka da zata kafa hukumar da zata ke saka ido kan harkokin yankunan da aka kwato.

Yanzu haka ma jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta dukufa wajen tantance yankunan da aka kwato, babban jami’in hukumar a jihar Adamawa Sa’adu Bello, yace yanzu hankula sun kwanta kuma jama’a na ci gaba da komawa garuruwansu.

Wannan kuma na zuwa ne yayin da hukumomin kasar Kamaru ke shirin mayar da yan Najeriya kusan Dubu 86 zuwa gida Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

JIhar Adamawa Zata Kafa Hukumar Da Zata Ke Saka Ido Kan Gururuwan Da Aka Kwato - 4'07"