Jeff Sessions Atoni Janar Na Amurka Ya Bude Wa Shugaba Trump Ido

Atoni Janar na Amurka Jeff Sessions

Biyo bayan caccakar da Shugaba Trump ya ci gaba da yi masa, Atoni Janar Jeff Sessions ya sha alwashin yin aikinsa da adalci tare da kare doka da kundun tsarin mulkin kasar duk ba sani ba sabobalantana sauya wani abu domin shugaban kasa

Atoni Janar na Amurka Jeff Session ya yiwa shugaba Donald Trump tsayin daka jiya Laraba bayanda Trump ya ce abin kunya ne da Sessions ya yi kira da a gudanar da bincike na cikin gida kan yadda jami'an shari’a suka nemi izinin sawa tsohon hadimin yakin neman zaben Trump ido.

A wata ja in ja ta ba sabanba a bainar jama'a tsakanin shugaban Amurka da daya daga cikin jami'an majalisar zartaswar da ya zaba,Sessions ya ce zaben babban jami'in ma'aikatar shari'a ya gudanar da binciken abu ne da ya dace domin tantance ko hukumar bincike manyan laifuka ta Amurka ta yi ba daidai ba yayin neman izini daga kotu na sawa tsohon hadimin Trump Carter Page ido.

Sission ya ce, muddin shi ne babban lauyan gwamnati zai ci gaba da gudanar da aikisa da mutumci, kuma ma'aikatar zata ci gaba da gudanar da ayyukanta ba sani ba sabo bisa ga kundin tsarin mulkin kasa.

Trump ya shafe watanni yana yiwa Sessions shagube sai dai bai kore shi ba, tunda Session ya janye kansa daga sa ido kan hukumar dake binciken batun katsalandan da da ake zargin Rasha da yi a zaben shugaban kasa na shekarar 2016, sabili da huldarsa da jakadan Rasha a Amurka, Sergey Kislyak, a lokacin yakin neman zabe. Janye kansa da Session ya yi daga batun ya sa aka zabi Robert Mueller ya shugabanci kwamitin bincike na musamman, wanda binciken da yake gudanarwa kan alakar ofishin yakin neman zaben Trump da Rasha ya dabaibaye gwamnatin Trump.