Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Ta Hannun Daman Shugaba Trump Ta Gurfana A Majalisar Dokokin Kasar


Hope Hicks babbar daraktar sadarwa ta Shugaban Amurka Donald Trump
Hope Hicks babbar daraktar sadarwa ta Shugaban Amurka Donald Trump

A halin da ake ciki, wata darektar yada labaran shugaban Amurka Donald Trump mai suna Hope Hicks, wadda ta jima tana aiki tare da shi, a jiya Talata ta bayyana gaban kwamitin majalisa mai binciken alakar kwamitin yakin neman zaben Trump da kasar Rasha, sai dai ta ki bada amsar wasu tambayoyi da 'yan majalisar suka yi mata a kan aikinta na tsawon watanni 13 a fadar White House.


Kwamitin kula da ayyukan leken asiri na majalisar dattawa ya gana da Hicks a asirce, wacce a farko take aiki da iyalan Trump a matsayin jami’ar hulda da jama’a kuma mai magana da yawun 'yar Trump, Ivanka Trump, domin tallatar da kasuwancin ta sutura, kafin daga bisani ta shiga kwamitin yakin neman zaben Trump da yayi nasarar lashe zaben.


Kafin fara sauraren bahasin, dan majalisa Chris Stewart, dan jam'iyyar Republican daga jihar Utah, ya fadawa manema labarai cewa Hicks zata ki amsa wasu tambayoyi a kan aikinta na White House. An kwashe sa’o’i da dama wurin saurarenta amma ba a iya gane tambayoyi da Hicks take niyyar amsawa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG