Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Bayyana Yiwuwar Tattaunawa Da Koriya ta Arewa


Donald Trump, shugaban Amurka
Donald Trump, shugaban Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yiwuwar tattaunawa da Koriya ta Arewa idan an samu yanayin da ya dace, wato Koriyan ta yi watsi da shirin nukiliyarta, yin hakan zai samar da yanayin da ya dace

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yiwuwar tattaunawa da Koriya ta Arewa, amma sai an sami yanayin da ya dace, yayinda yake gargadi da cewa, idan Pyongyang bata yi watsi da ayyukanta na nukiliya da makamai masu linzami ba, akwai yiwuwar a yi gagarumin rasa rayuka, da ba a taba zato ko tsammani ba.

Trump ya bayyana haka ne jiya Litinin a fadar White House yayinda yake ganawa da gwamnonin jihohin Amurka inda ya ambaci tayin da Koriya tayi kwanan baya ta bakin shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in, da yace “suna so su tattauna da Amurka."

Zamu ga abinda zai faru, inji shugaba Trump, yace tilas ne a dauki matakin da zai kawar da barazanar da makaman kare dangin Koriya ta Arewa ke yiwa Amurka da kawayenta.

Yayin ganawa da manema labarai na fadar White House, kakakin fadar Sarah Huckabee Sanders ta ce tilas ne kawar da makaman nukiliya daga yankin kasashen Koriya ya zamo sakamakon duk wata tattaunawa da za a iya yi da Koriya ta Arewa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG