Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Dake Kare Hakkin Dan Adam Ta Amurka, ACLU Ta Kai Trump Kara Kotu


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Hukumar kare hakkin dan Adam ta nan Amurka zata kai shugaban Amurka Donald Trump kara kotu saboda raba wata yarinya 'yar shekaru bakwai da mahaifiyarta bisa zargin sun shigo kasar daga Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ba tare da izini ba

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Amurka da ake kira ACLU a takaice, zata yi karar gwamnatin shugaba Trump sabili da raba wata karamar yarinya ‘yar shekaru bakwai ‘yar ci rani daga Damokaradiyar Jamhuriyar Congo da mahaifiyarta.

Karamar yarinyar da ta kidime da ake kira S.S tana zaune a wajen tsare mutane dake birnin Chicago, yayinda mahaifiyarta da hankalinta yake tashe Ms. L take hannun hukuma a San Diego dake tazarar kilomita dubu uku da dari biyu daga inda diyar take. Sun yi Magana ta wayar tarho ne kadai a wadansu lokuta.

Kungiyar ta bayyana raba uwar da ‘yarta a matsayin abinda ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma hankali, tana kuma kira da a sake su ko kuma a tsare su a wuri daya.

An bayyana cewa macen da ‘yarta sun shiga San Diego ne suna neman mafaka daga tashin hankalin da ake yi a Damokaradiyar jamhuriyar Congo, suna kuma fargabar abinda zai faru da su idan aka tilasta su komawa kasarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG