Janar Ihejirika da Modu Sherrif su na ci Gaba da Musanta Goyon Bayan Boko Haram

Sanata Ali Modu Sheriff.

A yayin da rundunar sojan Najeriya ta bakin kakakinta Janar Chris Olukolade take kara jaddada cewa manyan kwamandoji su na rike da rundunoninsu daram.

A yayin da rundunar sojan Najeriya ta bakin kakakinta Janar Chris Olukolade take kara jaddada cewa manyan kwamandoji su na rike da rundunoninsu daram, har yanzu ana ci gaba da tayar da kura game da kalamun da wani mai shiga tsakani a tattaunawar neman sako daliban Chibok yayi kan wadanda ke daure ma Boko Haram gindi.

Stephen Davis, dan kasar Australiya, ya bayyana cewa tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Azubuike Ihejirika, da tsohon gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sherrif, sune wuka da nama a Boko Haram.

Janar Ihejirika, ya karkata fusatarsa a kan tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Nasir el-Rufa'i, wanda shi ya fara yayata labarin wannan hirar da wani gidan telebijin yayi da mai shiga tsakanin a kasar Australiya, inda a ciki ya bayyana wannan zargin.

Shi kuma da yake musanta wannan zargin da aka yi masa, tsohon gwamna Mou sherrif, yace zai shigar da karar Mr. Davis a gaban kotu a Britaniya, bisa zargin bata masa suna. Yace wannan zargin da ake yi masa ba ya da tushe.