A jana'izar marigayin da aka yi a Babban Masallacin kasa da ke Abuja, dumbin Jama'a ne suka halarta daga ciki da wajen birnin.
Janar Alkali, wanda ya bar Abuja zuwa Bauchi, wasu yan ina da kisa ne suka halaka shi a Dura Du da ke yankin karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato. Sun yi wani kabari mara zurfi su ka binne shi ciki, kafin daga bisani suka cire gawar suka jefa ta a rijiya.
Sojojin Runduna ta uku sun kaddamar da binciken kwakwaf inda aka gani gawar cikin Rijiyar.
Sanata Mohammed Hassa da ke wakiltar shiyyar Patiskum a Jihar Yobe inda Janar Alkalin ya fito ya nemi gwamnatin tarayya ta kaddamar da bincike don gano Wadanda suka tafka wannan aika-aika a hukunta su.
Yace Yankin Jos yanzu ya zame wuri Mai hadarin gaske ga matafiya da suka fito ko suka nufi jihohin dake Arewa maso gabas Al'amarin da ya sa dole Suke zagayawa ta Kaduna-Kano yayin tafiye tafiye su.
Shi ma Mallam Ibrahim musa Wanda ya ce kashe Janar Alkali babbar hasara ce ga baki dayan Najeriya, don haka akwai bukatar a hukunta duk masu hanu cikin wannan ta'addanci don ya zame aya ga wasu tsageru na gaba.
Ga wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5