A yau kwamitin da majalisar dokokin jihar Kano ta kafa domin bincikar zargin karbar rashawa da ake yi wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya yi zamansa na biyu inda aka gayyaci gwamnan da ya bayyana a gaban kwamitin.
Sai dai Ganduje bai halarci zaman na yau Juma’a ba, amma ya tura kwamishinan labaran gwamnatin Kano, Malam Muhammadu Garba.
“Kowa ya riga ya san cewa gwamna gogaggen ma’aikaci ne, saboda haka, ba zai yi irin wannan kuskuren na a zo a ce har za a ba shi cin hanci ko kuma na goro ba.” Inji Malam Garba, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, bayan da gabatar da takardun bahasinsu ga kwamitin.
Ya kara da cewa, “duk abin da majalisar za ta yi domin ta tabbatar da gaskiya, ina mai tabbatar maka da cewa gwamnati na tare da majalisa.”
Shugaban kwamitin, Hon. Babba Bappa Dan Agundi, ya ce babu dama su yi tambayoyin neman karin haske ga wakilin gwamnan tun da shi Gandujen bai samu halartar zaman ba amma ya ce za su yi dubi kan hoton bidiyon.
“Za mu duba wannan bidiyo da aka bayar ranar Talata, za mu yi hakan da lauyan Ja'afar Ja'afar da na mai girma gwamna” da kuma kwararru da za su iya tantance sahihancin wannan bidiyo.
Wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari, ya ce a jiya Alhamis wani sabon bidiyo ya sake fita kan zargin karbar rashawar, amma kuma Ja'afar ya nesanta kan shi da wannan bidiyo na baya-bayan nan.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum