Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Yin ‘Yar Girgizar Kasa A Abuja


Wani gini da ya rushe da kansa a Abuja
Wani gini da ya rushe da kansa a Abuja

Wannan shi ne karo na biyu da girgizar kasar ke aukuwa a birnin na Abuja. A farkon watan Satumba an samu makamancin hakan a unguwar Mpape.

An sake samun wata ‘yar girgizar kasa a yankin Maitama da ke Abuja babban birnin Najeriya kamar yadda wasu jaridun kasar suka ruwaito.

Girgizar kasar ta auku ne da misalin karfe 12:26 na daren jiya wacce ta dauki tsawon kusan minti daya da karfin maki 3.0 kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Rahotanni su ce tuni ma’aikatar ma’adinai da bunkasa fannin karafa ta kaddamar da bincike domin gano musabbabin motsawar da kasar ta yi.

Wannan shi ne karo na biyu da wannan lamari ke faruwa. A farkon watan Satumba an samu makamancin hakan a unguwar Mpape da ke birnin na Abuja.

Dukkanin girgizar kasar biyu ba su haifar da wata barna ba.

Hukumomin Najeriya sun yi kira ga mazauna birnin da su kwantar da hankulansu yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG