Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Ma'aikatan Najeriya Ke Shirin Yi


Wani lokaci a bara da ma'aikatan Najeriya ke zanga wata zanga
Wani lokaci a bara da ma'aikatan Najeriya ke zanga wata zanga

Alkalin ya ce ya ba da wannan umurnin ne saboda a kaucewa mummunan tasirin da yajin aikin zai yi akan tattalin arzikin Najeriya, wanda aka shirya za a fara a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Wata kotu a Abuja, babban birnin Najeriya, ta ba da umurnin cewa kungiyar kwadagon kasar ta dakatar da yajin aikin take shirin shiga.

A mako mai zuwa gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar ke shirin shiga yajin aikin na gama-gari idan har ba a fara biyan ma’aikata N30,000.00 ba a matsayin albashi mafi karanci.

A yau Juma’a alkalin kotun ma’aikata, Justice Sanusi Kado, ya ba da umurnin a cewar jaridar yanar gizo ta Premium Times, bayan da gwamnatin tarayya ta shigar da kara.

Alkalin ya ce ya ba da wannan umurnin ne saboda irin mummunan tasirin da yajin aikin ka yi akan tattalin arzikin Najeriya, wanda aka shirya za a fara a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Kungiyar kwadagon tana so ne a fara biyan ma'aikatan N30,000.00 karkashin wata yarjejeniya da ta ce an cimma a tsakaninta da gwamnatin da bangaren ma’aikatu da kamfanoni masu zaman kansu.

A lokacin hada wannan rahoto, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC ba su ce uffan ba.

A farkon makon nan kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce za ta biya N22,500.00 tayin da kungiyoyi kwadagon suka ki amincewa da shi ba.

It kuwa gwamnatin tarayya ta hakikance cewa N24,000.00 za ta biya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG