Janar Babangida mai ritaya yayi wannan kiran ne dangane da harin da akai a babban masallacin Kano.
WASHINGTON, DC —
Tsohon shugaban kasan wanda yayi magana da wakilin Sashen Hausa ta woyar tarho, yace harin da aka kai a daya daga cikin manyan masallatan Kano ranar jumma'a, har mutane fiyeda dari suka halaka ya kada shi ainun.
Tsohon shugaban kasar yace akwai bukatar su tsoffin shugabanni da gwanoni da gwamnatin tarayya su hadu domin suyi shawarwari na neman hanyoyin magance wannan batu.
Da aka tambayeshi ko a ganinsa gwamnatin tarayya ta gaza ne, tsoshon shugaban kasar yace, baya jin haka, domin ko wace gwamnati data zo, akwai irin kalubale daban da take fuskanta, sabanin irin gwamnatin data shude.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5