Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Najeriya Ibrahim Babangida Ya Dawo daga Jinya a Kasar Jamus


Tsohon shugaban Mulkin Soja a Najeriya Janar Ibrahim Babangida.
Tsohon shugaban Mulkin Soja a Najeriya Janar Ibrahim Babangida.

Janaral Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB ya koma Najeriya daga kasar Jamus inda ya kwashi tsawon lokaci yana jinya

Janaral din da ya koma Najeriya karshen mako yace yanzu ya samu lafiya. Ya godewa wadanda suka nuna damuwa akansa.

Yace ya je neman lafiya kuma Allah cikin ikonsa ya bashi lafiyar. Yadda mutane suka dinga rubuta masa wasika ko aika sako ya nuna lallai yana nan tare da mutane sabili da haka yayi matukar godiya.

Janaral Babangida ya san halin da Najeriya ke ciki amma bai ce komi ba a siyasance saidai yace a wurin Muryar Amurka ya ji Abubakar Shekau yana magana.

A wani halin kuma yau shugaban kamfanin dake buga jaridar Leadershinp Sam Inda Isaiah zai gabatar da kansa a matsayin dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta APC a garin Minna.

Malam Yahaya Etsu daraktan fafitikar neman zaben Isaiah a jihar Neja ya bayyana dalilinsu na gudanar da taron a Minna maimakon Abuja. Kundun tsarin mulkin APC yace idan mutum zai fara gabatar da kansa a matsayin dan takara ya fara daga gida. Yin hakan ya nuna suna biyayya da kundun tsarin mulkin jam'iyyar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG