A karshen wannan taro da aka gudanar ranar Asabar, majalisar ta yanke shawarar cewa akwai yiwurar haramta sana’ar acaba, ko kuma kabu kabu a duk fadin Najeriya, da nufin samar da wani sabon tsarin sufurin jama’a mai inganci.
Ministan Sufuri a Najeriya Sanata Idris Umar ya amince da wannan mataki.
Alhaji Babangida Shehu Mai Hula, shine shugaban Hadaddiyar Kungiyar ‘Yan Achaba a Najeriya.
“Na dauki wannan labari, kamar kowane labari da gwamnati take da shi na bukatar cigaba”.
Wannan sana’ace dai da mutane keyi saboda neman abin da zasu ciyar da iyalinsu, idan kuma har gwamnati zata hana wanna sana’a to saita taimaka samarwa masu wata sana’a. ga hirar Halima Djimrao da Alhaji Babangida Shehu Mai Hula, shine shugaban Hadaddiyar Kungiyar ‘Yan Achaba a Najeriya.