Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Neja Ya Shiga Takarar Gwamna


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja.
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja.

Alhaji Umar Nasko tsohon shugaban ma'akatan gidan gwamnatin jihar Neja ya shiga takarar kujerar gwamnan jihar.

Tsohon shugaban ma'aikatan ya fito ne a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kamar yadda aka yi zato idan an yi la'akari da jawabin gwamnan jihar na kwana kwanan nan.

A jawabin da ya gabatar Alhaji Umar Nasko yace yana da basirar yin aiki na cigaban jama'a duk da karancin shekarunsa.Idan har jam'iyyar PDP ta bashi dama za'asha mamaki, inji Nasko.

Taron ya samu halartar kusan kowane jami'in gwamnatin jihar. Kuma kusan duk 'yan majalisar dokokin jihar suka kasance a wurin taron. Shugaban majalisar Adamu Usman yace su a jihar Neja suna tafiya tare da gwamnati domin haka suna rokon Allah ya basu sa'a.

Sakataren gwamnatin jihar Neja Alhaji Idris Ndako shi ya wakilci gwamna Babangida Aliyu a taron. Idan ba'a manta ba gwamnan ya fada can baya cewa Allah ya nuna masa Nasko ne ya kamata ya gajeshi. A taron gwamnan yace ga amana nan ya baiwa jama'a.

Tsohon gwamnan Bayelsa da wasu kusoshin PDP sun halarci taron. Yanzu dai an samu 'yan takara takwas ke nan da suka fito a jam'iyyar PDP.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG