Jamus Ta Lashe Kofin gasar Confederation Cup Ta Duniya A Kasar Rasha
'Yan wasan kwallon kasar Jamus na murna bayan da suka lashe kofin gasar nahiyoyi na wannan shekarar 2017 a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli na shekarar 2017 a garin Saint Petersburg dake Rasha.
Kafin a fara wasan karshe tsakanin Jamus da kasar Chile a gasar nahiyoyi ta Confederation Cup 2017 a ranar Lahadi 2 ga watan Yuni na shekarar 2017 a garin Saint Petersburg dake Rasha.
Dan wasan Brazil Ronaldo rike da kofin gasar ta Confederation Cup yayin da ake bikin rufe gasar a birnin St. Petersburg dake Rasha
'Yan wassan kwallo kafa na kasar Chile kafin a fara wasan karshe a babban fili na wasanni dake garin Saint Petersbourg dake Rasha a ranar Lahadi 2 ga watan Yuni shekarar 2017.
Dan wasan kwallon kasar Chili Alexis Sanchez a lokacin wasan karshe a filin wasanin kwallo dake Saint Petersburg dake Rasha, ranar Lahadi 2 ga watan Yuni shekarar 2017
Mai horar da 'yan wasan kasar Jamus Joachim Loew, yayin da ake shirin fara wasan karshe a filin wasanni na Sint Petersburg dake a Rasha, ranar Lahadi 2 ga watan Yuli na shekarar 2017.
Mai koyawa 'yan kasar Chile wasa, Juan Antonia Pizzi yayin da ake buga wasan karshe a filin Saint Petersburg dake Rasha, ranar Lahadi 2 ga watan Yuli na shekarar 2017.