Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun ICC Ta Nuna Gazawar Afirka Ta Kudu Kan Kin Kama Al Bashir


Shugaban Sudan Omar al Bashir da kotun ICC ke nema ruwa a jallo
Shugaban Sudan Omar al Bashir da kotun ICC ke nema ruwa a jallo

Har yanzu ziyarar da shugaban Sudan Omal al Bashir ya kai Afirka ta Kudu a 2015 na ci gaba da ta da kura, inda a baya-bayan nan, kotun hukunta manya laifuka ta ICC ta zargi Afirka ta Kudu da kin bin ka'idodin da suka rataya a wuyanta.

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ta zargi Afirka ta kudu da kin cika ka'idodin da suka rataya a wuyanta na kama shugaban Sudan, Omar al Bashir, wanda ake tuhuma da zargin aikata laifukan kisan kiyashi, zargin da al Bashir din ya dade yana musantawa.

Wani alkalin kotun ta ICC, Cuno Tarfusser, ya fada a yau Alhamis cewa matakin da Afrika ta Kudu ta dauka na kin kama shugaban Sudan din a lokacin da yake cikin kasarta, ya sabawa bukatun da kotun ta gabatar ga kasashen duniya na a kama shi.

Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta yi maza-maza ta goyi bayan matsayar da kotun ta ICC ta dauka, inda ta ce hakan na nufin al Bashir ba shi da rigar kariya da za ta hana a kama shi a ko'ina.

Ta kuma yi kira ga sauran kasashen duniya da kada su bi sahun abinda Afirka ta Kudun ta yi na kin kama shugaban na Sudan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG